Da yake Karin haske yayin a Mogadishu, babban birnin kasar ta Somaliya jakadan kasar Sin a kasar Somaliya Qin Jian ya bayyana kudurin kasarsa na taimakawa matakan da Somaliya ke dauka na samar da kayayyakin jin kai da galibi kananan yara da mata ke matukar bukata.
Jakada Qian ya ce, kasar Sin na fatan hada kai da asusun na UNICEF don kaiwa ga al'ummomin dake wurare masu wahalar shiga kuma ke cikin mawuyacin hali. Ya ce za a yi amfani da kudaden ne wajen sayen abinci mai gina jiki da magunguna don baiwa mutanen dake cikin hadari, ciki har da yara 15,000 wadanda ke fama da matsalar karancin abinci mai gina jiki sakamakon matsalar farin da ake fama da ita a wasu sassan kasar.
Alkaluman asusun na UNICEF sun nuna cewa, kasar dake yankin kahon Afirka na fama da matsalar jin kai ne sakamakon kanfon ruwan sama, lamarin da ya tilastawa jama'a barin muhallansu, barkewar cututtuka da matsalar abinci mai gina jiki, inda a halin yanzu mutane miliyan 6.2 ke bukatar taimakon jin kai, kuma miliyan hudu daga cikin wannan adadi kananan yara ne.(Ibrahim)