in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ta ware karin kudin don rage fatara
2017-06-13 09:48:43 cri
Gwamnatin tsakiya ta kasar Sin ta kara ware wasu yuan biliyan 30.7 kwatankwacin dalar Amurka biliyan 4.52, domin taimakawa wajen rage fatara.

Ma'aikatar kudi ta kasar da ta bayyana haka a jiya Litinin, ta ce wannan ya kawo kudin da aka ware na rage fatara a matakin kananan hukumomi a bana zuwa kusan yuan biliyan 86.1.

Gwamnatin kasar Sin dai ta lashi takobin kawar da fatara tsakanin jama'arta nan zuwa shekarar 2020, domin samar da al'umma mai matsakaicin ci gaba.

A shekarar 2016 kadai, kasar Sin ta taimaka wajen fitar da mazauna kauyuka miliyan 12.4 daga kangin talauci.

Zuwa karshen shekarar 2016, mutane miliyan 43.35 ne ke cikin fatara a kasar Sin. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China