in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An bayyana dabarun rage fatara yayin taron duniya kan rage radadin talauci
2017-05-27 13:53:29 cri

An gudanar da babban taron duniya kan rage radadin talauci na bana a ranar Juma'a wato 26 ga watan Mayu a birnin Beijing. Taron ya ja hankalin sama da mahalarta 100 daga kasashe 7, ciki har da jami'ai da wakilai daga hukumomin duniya da cibiyoyin ilimi da 'yan kasuwa da kungiyoyi masu zaman kansu. Inda suka yi tattaunawa mai zurfi kan yadda za a inganta harkokin rage talauci tare da kuma samun dabaru daga matakan kasar Sin, domin taimakawa kasashe masu tasowa samun hanyar kawar da talauci.

Taken taron shi ne, "lalubowa tare da musayar kudurorin shugabanci wajen rage talauci". An kuma bayyana sabbin dabaru tare da bada misali da nasarorin da aka samu. Wannan ya bayyana irin matakan da kasar Sin ta dauka da sauran kasashe ta fuska daban-daban.

Mataimakin ministan ofishin watsa labarai na kasar Sin Guo Weimin, ya ce matakan da kasar Sin ta dauka na rage talauci bangare ne na akidar tausayawa al'umma. Yana mai cewa, da mutane miliyan 700 dake fama da talauci a duniya, ya kamata kasar Sin ta dauki dabarar bada labarinta, ta yadda za a samu wani dandali na musayar bayanai tsakanin kasar Sin da al'umomin duniya.

Ya kuma jadadda rawar da fasahar sadarwa ta zamani za ta taka wajen rage talauci, ya na mai bada misali da runbun adana bayanai na ilimin rage talauci a duniya.

Wakilin hukumar kula da samar da abinci da harkokin noma ta duniya FAO a kasar Sin da Koriya ta arewa, Vincent Martin ya yi kira da aka kara hadin gwiwa tsakanin kasashe masu tasowa don kara kaimi ga shirin kawar da talauci a duniya.

Ya ce idan ana son a tafi da kowa da kowa, tare da cimma muradun ci gaba masu dorewa na 1 da na 2, dole ne a dauki muhimman matakan rage talauci sannan a gabatar da matakan da kasar Sin tare da wasu kasashe suka dauka na rage talauci ga sauran al'ummomin duniya. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China