in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
'Yan Nijeriya sama da 1,300 sun koma gida daga Libya
2017-12-16 12:30:00 cri

Hukumar ba da agajin gaggawa ta kasar Nijeriya wato NEMA, ta ce cikin kwanaki 10 da suka gabata, jimilar 'yan kasar 1,317 ne suka koma gida daga kasar Libya, bayan sun yi watangarari a kasar da ke arewacin Afrika a kan hanyarsu ta zuwa Turai.

Hukumar ta ce mutanen sun koma ne cikin kashi daban-daban, tsakanin ranar 5 zuwa 15 ga watan nan, da taimakon hukumar kula da masu kaura ta duniya wato IOM da gwamnatin Nijeriya da kuma kungiyar Tarayyar Turai.

Cikin wata sanarwa da ya fitar, shugaban hukumar NEMA Mustapha Maihajja, ya ce wasu 249 wadanda su ne kashi na karshe, sun isa birnin Lagos a ranar Alhamis da ta gabata.

Cikin watan Nuwamba kadai, 'yan Nijeriya 1,295 ne suka koma gida daga Libya, bayan sun bukaci hakan da kansu.

Jami'in ya ce, gwamnatin za ta ci gaba da aiki da hukumomin kasashen waje don tabbatar da wasu karin 'yan Nijeriyar su koma gida daga Libya, inda suke fuskantar matsananciyar wahala da take hakkokinsu. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China