Cikin sanarwar da ya fitar ta hannun kakakinsa Farhan Haq, Antonio Guterres ya yi wa iyalan wadanda suka mutu da Gwamnatin da al'ummar Nijeriya ta'aziyyar rashin da suka yi, yana mai yi wa wadanda suka jikkata fatan samun lafiya, inda kuma ya yi kira da a yi gaggawar hukunta wadanda ke da hannu wajen aikata mummunan aikin.
Antonio Guterres ya kuma jadadda goyon bayan MDD ga Gwamnatin Nijeriya a yaki da take da ta'addanci da masu kaifin ra'ayin addini, ya na mai sabunta kudurin majalisar na ci gaba da mara baya ga shirye-shiryen yaki da ta'addanci.
Wani dan kunar bakin wake ne ya tada bam yayin sallar asuba a wani masallacin garin Mubin jihar Adamawa a jiya Talata, al'amarin da ya yi sanadin mutuwar mutane 50. (Fa'iza Mustapha)