Ezra Sakawa, babban darakatan asibitin ya shedawa 'yan jaridu cewa, asibitin ya karbi mutane 48 wadanda harin ya shafa, 8 daga cikinsu sun mutu a yayin da ake duba lafiyarsu, kana mutane 15 an tura su zuwa asibitin gwamnatin tarayya dake Yola babban birnin jahar Adamawa.
Sakawa ya ce, ragowar mutanen dake kwance a asibitin suna cikin hayyacinsu kuma ana duba lafiyarsu.(Ahmad Fagam)