Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Adamawa Osman Abubakar ya bayyana a jiya cewa, an yi rikici a tsakanin Fulani makiyaya da manoma dake kauyuka biyu na yankin Numan na jihar Adamawa a daren ranar 20 ga wata, rikicin da ya haddasa mutuwar mutane 27, galibin su mata da kananan yara.
Rahotanni na cewa, wasu ganau sun bayyana cewa, mutane 9 sun bace a sakamakon rikicin. (Zainab)