in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sojojin Najeriya sun lalata wajen hada boma bomai na Boko Haram yayin wani hari ta sama
2017-11-23 09:57:22 cri
Rundunar sojin sama ta Najeriya ta bayyana cewa, dakarunta sun hallaka mayakan Boko Haram masu yawan gaske, kana sun lalata wani wajen da mayakan ke hada boma bomai, a lokacin da sojojin suka kaddamar da hare hare ta sama a jahar Borno dake arewa maso gabashin kasar a ranar Laraba.

Sanarwar da hukumar sojin ta fitar ta ce, an lalata wajen hada boma boman ne a dajin Yiwe, wanda ke da tazarar kilomita 23 a kudancin Konduga dake arewacin jahar.

Rundunar sojin saman ta ce, a sakamakon wani binciken sirri data gudanar a lokutan bayan ne, ta gano kayayyakin hada boma boman wanda mayakan Boko Haram ke amfani da su a wajen wanda ya kasance a matsayin maboyarsu, inda a wajen ne suke shirya dabarun kaddamar da hare haren ta'addanci.

A cewar hukumar sojin saman, daga wannan waje ne mayakan Boko Haram suka tsara kaddamar da harin tagwayen boma bomai na jahar Borno, wanda suka kaddamar a ranar 18 ga watan Nuwamba, inda yayi sanadiyyar hallakar mutane 5.

Hare haren ta sama ya lalata maboyar 'yan ta'addan, inda ya tarwatsa dukkan ababen fashewar da mayakan Boko Haram din suka jibge a yankin, yayin da wasu daga cikin 'yan ta'addan suka yi yunkurin tserewa, sojojin sun hallakasu ta hanyar amfani da wasu bindigogi da makaman roka, inji sanarwar sojin saman Najeriyar.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China