in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kwashe bakin haure sama da 70 da suka shiga Libya ba bisa ka'ida zuwa Nijar
2017-12-16 12:00:46 cri

Babbar hukumar kula da 'yan gudun hijira ta MDD ko UNHCR a takaice ta sanar a jiya Jumma'a cewa, ta yi nasara kwashe bakin haure 74 galibinsu mata da kananan yara daga kasar Libya zuwa Jamhuriyar Nijar.

Hukumar ta UNHCR ta ce, dukkan wadanda aka kwashe tare da taimakon abokan huldarta dake Jamhuriyar Nijar, 'yan kasashen Eritrea da Somaliya ne, kuma za a tsugunar da su a masaukan baki a birnin Niamey na Jamhuriyar Nijar.

Bugu da kari, hukumar ta ce, ta yaba da goyon bayan da hukumar kungiyar tarayyar Turai ta bayar a shirin da ta kira na ceton rai.

Haka kuma a jiya ne, kungiyar kula da kaurar jama'a ta duniya (IOM) ta ce, an tusa keyar wasu rukunonin bakin haure 718 da suka shiga kasar ta Libya ba bisa ka'ida ba zuwa kasashensu na asali.

Libya dai ta kasance matattarar bakin haure da ke fatan tsallaka tekun bahur Rum don shiga Turai, sakamakon matsalar tsaro da tashin hankali da kasar ta tsinci kanta a ciki. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China