in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kwashe daruruwan 'yan ci rani daga Libya
2017-12-09 12:40:39 cri

Hukumar dake lura da masu kaura ta kasa da kasa IOM, ta ce a ranar Alhamis din da ta gabata, masu shirin tafiya ci rani kasashen turai su 376 da suka makale a kasar Libya, sun amince a maida su kasashen su na asali.

Hukumar ta ce 'yan ci ranin sun karbi tallafin jin kai, tare da amincewa a mayar da su kasashen Gambia da Najeriya. Rahotanni sun bayyana cewa, a cikin wannan wata kadai, IOM na ci gaba da tallafawa 'yan ci rani da suka makale a Libya su kimanin 15,000, domin su samu zarafin komawa kasashen su.

Hukumar ta IOM ta kara da cewa, a wannan shekara ta 2017 kadai, bakin haure 14,754 daga kasashen Afirka 24, sun koma kasashen su na asali daga kasar ta Libya.

Tun a shekarar bara ne dai IOM da mahukuntan Libya, suka kaddamar da shirin bada taimakon jin kai ga 'yan ci ranin dake Libya, gabanin komawar su gida.

Libya dai ta zamo zangon dubban masu hankoron tsallakawa turai ta Bahar Rum, sakamakon karancin tsaro, da tashe tashen hankula dake addabar kasar, tun bayan juyin mulkin shekarar 2011, wanda ya kawo karshen gwamnatin tsohon shugaban kasar Muammar Gaddafi.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China