Kwamitin ya yi tir da wannan mummunar dabi'a wanda ya ce ta saba da hakkin dan Adam, ya na mai cewa ta na iya zama laifin take hakkin bil adama.
Kwamitin ya yi kira ga hukumomin da suka dace su gudanar da bincike kan lamarin ba tare da bata lokaci ba, domin tabbatar da kamawa da ganin wadanda ke da hannu sun fuskanci shari'a.
Kwamitin ya kuma jadadda cewa, ya damu da safarar 'yan gudun hijira da sauran mutane, ya na mai maraba da ayyukan shirin majalisar mai bada tallafi a Libya, wajen shirawa da samar da agajin jin kai ga 'yan gudun hijira da 'yan ci rani. (Fa'iza Mustapha)