in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Libya ta tsaurara matakan dakile safarar bil adama
2017-12-11 11:03:30 cri
Jami'an sojin kasar Libya sun tabbatarwa kamfanin dillancin labaran Xinhua cewa, a ranar Lahadi dakarun tsaron kasar suka fara wani aikin sintiri a kudu maso gabashin iyakar kasar domin dakile masu fasa kwauri da kuma safarar bil adama.

Saeed Wanis, wani jami'in sojin Libya ne ya shedawa Xinhua cewa, tuni bataliyar sojoji ta Subul Assalam ta fara aikin sintiri a kudu maso gabashin birnin Kufra.

Wanis yace, aikin sintirin don bankado masu aikita laifukan fasa kwauri a yankunan kasar ta Libya yana fama da manyan kalubaloli, sakamakon wahalhalun da ake tunkara wajen shiga yankunan wadanda suke da girma da kuma yanayi na sahara, kuma yankin na bukatar adadin jami'an soji masu yawa.

Bataliyar sojin ta fitar da wata sanarwa a ranar Asabar game da barazanar masu aikata laifin safarar bil adama da masu fasa kwarin man fetur, inda rundunar ta bada tabbacin cewa ba zata taba lamintar ayyukan masu fasa kwaurin ba, kuma dakarun sojin zasu cigaba da yin sintiri a cikin sa'oi 24 a kullum.

Kudancin kasar Libya yana fama da matsalolin masu fasa kaurin man fetur da matsalar bakin haure, sakamakon matsalar tabarbarewar al'amurran tsaro da ake fama da shi a yankin.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China