in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Taron EU da AU ya amince a kwashe bakin hauren da suka makale a Libya
2017-11-30 20:08:40 cri
Shugaba Emmanuel Macron na kasar Faransa ya bayyana cewa kasashen Turai da na Afirka guda 9 gami da kungiyar tarayyar AU da takwararta ta Turai(EU) da kuma MDD, sun yanke shawarar hanzarta kwashe bakin hauren da suka makale a kasar Libya zuwa kasashensu na asali.

Macron wanda ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai bayan kammala wani taron kolin gaggauwa da aka bude tsakanin kungiyar AU da EU a birnin Abdijan cibiyar kasuwancin kasar Cote d'Ivoire, ya ce rahotanni da gidan talajibin na CNN ya nuna game da yadda ake sayar da bakin haure 'yan Afirka kamar bayi a Libya, a kan hanyarsu ta zuwa Turai ya girgiza kasashen na Afirka, lamarin da ya haifar da kiraye-kiraye daga shugabannin da suka halarci taron kolin.

Shugaba Macron ya ce, nan da 'yan kwanaki ko makonni za a fara kwashe 'yan ciranin da suka makale, inda ya yi kira da a hukunta masu fataucin bil-Adama dake da alaka da kungiyoyin 'yan ta'adda.

A jawabinsa na bude taron shugaba Alassane Ouattara na Cote d'Ivoire, ya yi kira da a kawo karshen wannan tsohuwar ta'ada.

MDD, da kungiyoyin AU da EU da kasashe kamar Jamus da Italiya da Sifaniya da Faransa da Chadi da Nijar da Jamhuriyar Congo da kuma Morocco, sun goyi bayan kwashe bakin hauren da suka makale a kasar ta Libya.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China