in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mahukuntan kasar Libya sun sha alwashin hukunta masu hannu a cin zarafin 'yan ci rani
2017-12-15 13:54:21 cri

Mataimakin firaministan kasar Libya tsagin da MDD ke goyon baya Ahmad M'etig, ya ce ko shakka babu za a hukunta wadanda ke da hannu a cin zarafin bakin haure dake shiga kasar Libya ba bisa ka'ida ba.

A kwanan baya ne dai wani bincike da gidan talabijin na CNN ya yi, ya nuna yadda ake gwanjon bakin haure da suka shiga kasar ta Libya, inda aka nuna yadda ake sayar da irin wadannan mutane kan kudi da bai wuce dalar Amurka 400 ba.

Ahmad M'etig ya ce a matsayin su na jagororin hukumar zartaswar gwamnatin kasar Libya, sun riga sun kafa kwamitin bincike, domin gano gaskiyar zarge zargen da aka yi game da cinikin bayi a Libya, kamar dai yadda kafofin watsa labaran yammacin duniya suka yayata a 'yan kwanakin baya.

Ya ce tabbas za a hukunta duk wanda aka samu da hannu a aikata wannan mummunan laifi, duba da cewa aikata hakan ya sabawa dokokin kasar Libya, da ma koyarwar addinin musulunci.

Sassan da aka dorawa alhakin gudanar da binciken a cewar Mr. M'etig, sun hada da ofishin babban mai gabatar da kara na kasar, da ma'aikatar harkokin cikin gidan kasar, da kuma hukumar dake yaki da kwararar bakin haure cikin kasar.

Kasar Libya dai ta zama wani sansani na dandazon 'yan ci rani, wadanda ke fatan tsallakawa turai ta tekun Bahar Rum, sakamakon kalubalen tsaro da kasar ta fada, tun bayan kifar da gwamnatin tsohon shugaban ta Muammar Gaddafi a shekarar 2011.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China