in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yawan kudin da aikin samar da hidima ga sassan harhada magunguna a Sin zai samar nan da shekara 2022 zai kai dala triliyan 1.5
2017-11-08 10:08:05 cri

Wani rahoto ya bayyana cewa, yawan kudin da aikin samar da hidima ga sassan harhada magunguna a Sin zai samar nan da shekara 2022 zai kai dala triliyan 1.5.

A wani rahoton da aka fitar game da aikin tare da hadin gwiwar cibiyar nazari kan fasahar, da cibiyar samar da bayanai ta Chengdu, dake karkashin cibiyar nazarin kimiyya ta kasar Sin ne, sun bayyana cewa, tun daga shekarar 2011, aikin samar da hidima ga sassan harhada magunguna a kasar Sin yana samun karuwar sama da kashi 15 bisa 100.

A shekarar da ta gabata, yawan kudin da aikin samar da hidima ga sassan harhada magunguna a kasar Sin ya kai kusan yuan triliyan 4, inda aka yi kiyasin shi ne karuwa mafi girma da aka samu a duniya baki daya.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China