in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kaddamar da gidauniyar dala biliyan 1.72 don tallafawa al'ummar Sudan ta Kudu
2017-12-14 11:32:48 cri
Ofishin MDD mai lura da ayyukan jin kai ko OCHA a takaice, da hadin gwiwar kungiyar samar da tallafin jin kai ta kasar Sudan ta kudu, sun kaddamar da gidauniyar dala biliyan 1.72, don tallafawa al'ummar Sudan ta Kudu wadanda tashe tashen hankula da yunwa suka shafa.

Da yake tsokaci game da hakan yayin wani taron manema labarai, mataimakin kakakin babban magatakardar MDD Farhan Haq, ya ce tun daga watan Disambar shekarar 2013 Sudan ta kudu ke fama da rigingimu, lamarin da ya tilasawa mutane da yawan su ya kai miliyan 4 tserewa gidajen su, ciki hadda wasu miliyan 1.9 dake zaune a cikin kasar, da kuma kusan miliyan 2 da suka tsallake zuwa sansanonin 'yan gudun hijira dake kasashe makwafta.

Mr. Haq ya kara da cewa, ci gaba da aukuwar tashe tashen hankula a kasar, ya haifar da karuwar yunwa, da rashin isasshen abinci mai gina jiki, da tasirin fari da ke barazana ga rayukan dubban al'ummar kasar

A wani ci gaban kuma, babban kwamishinan MDD mai lura da al'amuran 'yan gudun hijira Filippo Grandi, ya ce shekaru 4 tun bayan barkewar yakin basasa a Sudan ta kudu, a halin da ake ciki yanzu, kasar na bukatar taimakon gaggawa daga dukkanin sassa na kasa da kasa, ta yadda za a kai ga kawo karshen tsanantar halin jin tsakanin al'ummun kasar.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China