in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sudan da Sudan ta Kudu sun yi alkawarin ba za su ba da mafaka ga kungiyoyinn 'yan tawaye ba
2017-11-02 14:21:21 cri

Shugabannin kasashen Sudan da Sudan ta Kudu, sun yi alkawarin ba za su mara baya ko ba da mafaka ga kungiyoyin dake adawa da gwamnatocin su ba, sun jadadda kudurinsu na kiyaye yarjejeniyar da suka rattabawa hannu.

Yayin wata ganawa tsakanin shugaban kasar Sudan Omar al-Bashir da takwaransa na Sudan ta Kudu Salva Kiir Mayardit, shugaba al-Bashir ya bayyana shawa'ar kasarsa ta warware batutuwan dake ciwa kasashen 2 tuwo a kwarya ta hanyar hawa teburin sulhu.

A nasa bangaren, Salva Kirr ya yi alkawarin kasarsa ba za ta goyi bayan ko ba da mafaka ga kungiyoyin siyasa dake adawa da gwamnatin kasar Sudan ba.

Shugaban na Sudan ta Kudu, ya kuma jadadda aniyar gwamnatinsa ta aiwatar da kunshin yarjejeniyar zaman lafiya da ta cimma da bangaren dake adawa da ita, yana mai cewa, sun kuduri niyyar aiwatar da yarjejeniyar da suka rattabawa hannu a watan Agustan 2015.

Khartoum da Juba sun dade suna nunawa juna yatsa dangane da batun goyon baya ko ba da mafaka ga bangarorin adawa masu dauke da makamai.

A jiya Laraba ne Salva Kiir ya isa Sudan a wata ziyarar aiki ta yini biyu dake da nufin ganin an aiwatar da yarjejeniyar hadin kai da kasashen biyu suka cimma. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China