in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An yi arangama tsakanin SPLA da masu tsaron lafiyar tsohon babban hafsan sojojin Sudan ta kudu a Juba
2017-11-06 10:08:53 cri

Sojojin Sudan ta kudu sun bayyana fargabar cewa, fito na fiton dake faruwa tsakanin sojojin kwatar 'yancin Sudan (SPLA) da masu tsaron lafiyar tsohon babban hafsan sojojin kasar a Juba Paul Malong Awan na iya rikidewa zuwa tashin hankali.

Mai magana da yawun sojojin Sudan na SPLA Lul Ruai Koang ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, rikicin ya faru ne bayan da tsohon babban hafsan sojojin kasar mai fada a ji ya ki amincewa masu tsaron lafiyarsu su mika makamansu, lamarin da ya haifar da zaman zullumi a birnin Juba tun a ranar Asabar, inda sojoji suka toshe manyan hanyoyin dake birnin, ciki hadda hanyar zuwa filin saukar jiragen sama, har ma suka kewaye gidan Malong.

Koanga ya ce, gwamnati ta bukaci Malong da ya rage yawan masu tsaron lafiyarsa zuwa mutum uku, amma ya ki amincewa da wannan shawara, wannan ya sa aka tura sojoji gidansa don magance duk wani rashin jituwa da ka iya kaiwa ga tashin hankali.

Ya kara da cewa, gwamnati ba ta da wata niyya ta dagula lamarin. Kuma yanzu haka ana tattaunawa tsakanin gwamnati da janar Paul Malong a wani mataki na kawo karshen rashin fahimtar dake tsakanin sassan biyu.

Kafin shugaba Kiir ya kore shi a watan Mayun wannan shekara, ana kallon Malong a matsayin babban na hannun daman Kiir, kana mutumin da ya hada wata mayakan kabilarsa domin su yaki gwamnatin Salva Kiir.

Kungiyoyin kare hakkin dan-Adam sun sha zargin Malong da magoya bayansa da cin zarafin fararen hula a sassa daban-daban na kasar da yaki ya daidaita.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China