in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD ta yi gargadi game da tabarbarewar tsaro a Sudan ta Kudu
2017-12-08 09:35:47 cri
Mataimakin Sakatare Janar na MDD kan harkokin wanzar da zaman lafiya Jean Pierre Lacroix, ya yi gargadi game da tabarbarewar yanayin tsaro a Sudan ta Kudu, ya na mai kira ga Kwamitin Sulhu na MDD ya kara sa ido.

Jean Pierre Lacroix, ya ce sun damu kwarai da tabarbarewar tsaro dake kara kamari a Sudan ta kudu. Ya ce yayin da aka shiga lokacin hunturu, akwai yiwuwar rikicin dake tsakanin sojoji da kuma wanda ke kabilun kasar ya ta'azzzara.

Ya kuma bukaci kwamitin sulhun ya kara kaimi wajen ganin an sulhunta rikicin a siyasance.

Jim kadan bayan samun 'yancin kai a shekarar 2011 ne, Sudan ta Kudu ta fantsama cikin yakin basasa, inda aka yi kiyasin mutane 300,000 sun mutu tun daga karshen shekarar 2013. Sannan, sama da mutane miliyan 1.5 ne suka tsere zuwa kasashen makwabta, galibi kuma na gudun hijira a cikin kasar. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China