in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD ta bayyana damuwa game da sabon tsarin izinin aiki na Sudan ta Kudu
2017-11-08 10:16:47 cri

Hukumar ba da agajin jin kai ta MDD dake aiki a Sudan ta Kudu, ta bayyana damuwa game da tashin kudin neman izinin aiki ga baki tare da wa'adin wata guda da gwamnatin kasar ta ba baki don samun izinin aikin.

Shugaban ofishin kula da harkokin agajin jin kai na MDD a Sudan ta Kudu Ian Ridley, ya ce sabon kudin samun izinin aikin da sauran wasu kudade da aka sanya a watan Satumba, za su karawa hukumomin agaji na ciki da wajen kasar tsadar kai dauki ga mutane masu bukata.

Ofishin ya jadadda cewa, dole ne hukumomin ba da agajin dake aiki a Sudan ta Kudu su mutunta dokokin kasar, sai dai aiwatar da wasu dokoki masu sarkakiya na zama kalubale ga kungiyoyi masu zaman kansu da sauran hukumomi.

A ranar Litinin da ta gabata ne hukumar ba da agajin gaggawa ta Sudan ta Kudu, ta ce ta gano sama da baki 1,000 dake aiki da hukumomin ba da agaji a kasar ba tare da izini ba, inda ta ba su wa'adin wata guda su samo izinin aiki ko su fuskanci tuhuma. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China