in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Sudan ta kudu zai ziyarci Sudan
2017-10-30 09:59:27 cri

Shugaba Salva Kiir Mayardit na kasar Sudan ta kudu, zai gudanar da ziyarar aiki ta yini biyu a kasar Sudan, inda ake sa ran zai zanta da shugaban kasar Omar al-Bashir, ya kuma sanya ido ga rattaba hannu kan wasu yarjeniyoyi da suka shafi kasashen biyu.

Ana kuma sa ran shugaba Kiir zai gudanar da shawarwari tare da mataimakin shugaban kasar Sudan na daya kuma firaministan kasar Bakri Hassan Saleh

A daya hannun kuma, tawagar ministocin sa za su zanta da takwarorin su na kasar Sudan, game da batutuwa daban daban da suka shafi ci gaban sassan biyu.

Sudan da Sudan ta kudu dai sun gaza aiwatar da yarjejeniyar da suka kulla cikin watan Satumbar shekarar 2012 a birnin Addis Ababa na kasar Habasha, bisa kulawar kungiyar hadin kan Afirka ta AU.

Yarjejeniyar dai ta kunshi batutuwa masu alaka da tsaro, da matsayin 'yan kasa, da batun kan iyakokin kasashen biyu, da tattalin arziki, da sauran batutuwa masu alaka da cinikayyar mai, da hada hadar kasuwanci.

Sai dai kuma waccan yarjejeniyar ba ta kunshi shata kan iyakar yankin nan na Abyei mai arzikin mai da kasashen biyu ke takaddama a kan sa ba.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China