Wannan ya kasance karo na 14 da gwamnatin kasar Sin ta fitar da takardarta ta farko, da ta shafi harkokin raya kauyuka da aikin gona, da kuma bunkasa rayuwar manoma tun bayan da aka shiga sabon karni.
Takardar ta kuma jaddada cewa, bunkasa gyare-gyaren tsarin aikin gona, na bukatar wani dogon lokaci, ana kuma bukatar a daidaita huldar da ke tsakanin gwamnati da kasuwanni, da kuma daidaita moriyar sassa daban daban. Don haka ta ce kamata ya yi a fuskanci kalubalen da aka sanya gaba, don ingiza gyare-gyaren. (Lubabatu)