in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Namibiya za ta yi hadin gwiwa wajen samar da makamashi mai tsabta
2017-07-20 10:57:29 cri

Shugaban kasar Namibiya Hage Geingob, ya fada cewa kasarsa tana neman abokan hadin gwiwa da ba su shawarwari game da yadda za ta yi amfani da makamashi mai tsabta.

Shugaba Geingob ya bayyana hakan ne a lokacin da yake ganawa da tsohon shugaban kasar Ghana John Mahama a Windhoek.

Ya ce, akwai babbar matsala dake damun kasar tasa. Kuma a cewar sa hakika kasar na bukatar lalibo hanyoyin da za ta bi domin magance ta.

Ya ce, kasar Namibiya tana da dukkan hanyoyin samar da makamashi mai tsabta, ciki har da ma'adanin Uranium.

Don haka ya ce suna bukatar neman mutanen da za su yi hadin gwiwa tare, kuma su ba su shawarwari.

Mahama ya ziyarci Namibiya ne a madadin bankin raya ci gaban Afrika wanda ya kebe kasar da cewa tana daya daga cikin kasashen da za su iya samar da makamashin lantarki domin amfanin kasar har ma da baiwa kasashen waje.

Ziyarar ta Mahama ta zo ne, a daidai lokacin da bankin na AfBD ya ware wasu kasashen Afrika a matsayin kasashen da za'a samar da makamashi mai tsabta.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China