in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
UNHCR: Jamhuriyar dimokuradiyyar Congo na da masu gudun hijira miliyan 3.9
2017-10-24 20:58:44 cri

Hukumar dake kula da 'yan gudun hijira ta MDD UNHCR, ta nuna matukar damuwa game da karuwar al'ummomin dake kauracewa gidajen su a jamhuriyar dimokuradiyar Congo.

Kakakin hukumar ta UNHCR Adrian Edwards ne ya bayyana hakan a Talatar nan, inda ya ce a yanzu haka, yawan mutane dake kauracewa gidajen su a cikin sassan kasar daba daban, ya kai mutum miliyan 3.9, adadin da ya ninka wanda ake da shi a shekarar 2015.

Mr. Edwards wanda ke bayyana hakan yayin wani taron 'yan jaridu, ya ce a cikin watanni 3 da suka gabata, mutane 428,000 sun gujewa muhallansu, kuma a tsawon shekara guda, 'yan kasar kimanin 100,000 sun tsallaka iyaka zuwa makwabtan kasashe domin neman mafaka.

Ya ce bisa jimilla, yanzu haka akwai 'yan Congon kimanin 621,711 dake fakewa a kasashen Afirka sama da 11, don haka akwai matukar bukatar kudaden samar musu da tallafi.

Tashe tashen hankula masu nasaba da kungiyoyin 'yan ta da kayar baya dai na rura wutar kabilanci da siyasa, lamarin dake sabbaba fadace fadace a sassan daban daban na kasar, kuma akwai yiyuwar ci gaba da fuskantar matsalar rabuwar al'ummomi da muhallansu a wurare da dama a nan gaba.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China