in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Syria ta yi kira ga MDD ta rushe rundunar hadin gwiwa da Amurka ke jagoranta saboda take hakkin fararen hula da take yi
2017-08-07 10:27:38 cri
Ma'aikatar harkokin wajen Syria, ya sake sabunta kira ga MDD da ta rushe rundunar hadin gwiwa ta yaki da ta'addanci da Amurka ke jagoranta, saboda laifukan da take aikatarwa kan fararen hula.

Kamfanin dillancin labarai na SANA ya ce ma'aikatar ta yi kiran ne a jiya, inda ta ce salon kisan kiyashin da Amurka ke wa fararen hula ya saba da dokokin kasa da kasa, tana mai bukatar a gaggauta rushe rundunar da aka kafa ba tare da bukatar kasar ba, wanda kuma ba ya cikin tsarin MDD.

Ma'aikatar ta bada misali da mabambantan lokuta da fararen hula suka jikkata, sanadiyyar luguden wuta da rundunar ke yi ta sama, tana mai cewa, Amurka ta yi amfani da sinadarin farin Phosphorus a wani hari da ta kai wa fararen hula a birnin Raqqa dake arewacin kasar.

Haka zalika, hare-haren sun lalata gidaje da asibitoci a Raqqa, babban birnin kungiyar IS na asali.

Ma'aikatar ta kara da cewa, rundunar ta kara aikata irin wadancan laifuka a lardunan Hasakah da Aleppo da Deir al-Zour.

Kiran na Syria, na zuwa ne kwana guda, bayan mutane 43 sun mutu a wuraren daban-daban na birnin Raqqa, sanadiyyar luguden wuta da rundunar hadin gwiwa da Amurka ke jagoranta ta yi. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China