in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin na fatan ganin an warware takaddamar siyasa a Zimbabwe cikin lumana
2017-11-16 09:08:23 cri

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Geng Shuang, ya ce Sin na fatan ganin an warware takaddamar siyasa da ta kunno kai a Zimbabwe cikin lumana.

Yayin wani taron manema labarai da ya gudana a jiya Laraba, Mr. Geng ya amsa tambayar manema labarai game da halin da ake ciki a Zimbabwe, inda ya ce Sin na bibiyar halin da ake ciki a kasar sau da kafa.

Mr. Geng ya kara da cewa, wanzuwar zaman lafiya da lumana, tare da bunkasar ci gaba a Zimbabwe, ya dace da bukatun kasar, da ma makwaftanta dake yankin ta, kuma buri ne na sauran kasashen duniya kawayenta. (Saminu Hassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China