in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaba Xi ya aike da sakon jaje ga shugaba Trump bisa harin bindiga da aka kai jihar Texas
2017-11-07 08:48:08 cri
Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya aike da sakon jaje ga takwaransa na Amurka Donald Trump, bisa harin bindiga da aka kai jihar Texas, al'amarin da ya yi sanadin mutuwar mutane 27 tare da raunata wasu a kalla 20.

Xi Jinping ya bayyana alhini kan harin da aka kai wa wadanda ba su ji, ba su gani ba, yana mai jajantawa iyalan wadanda suka mutu da wadanda suka jikkata, tare da yi musu fatan samun lafiya cikin gaggawa.

An kai harin na bindiga ne da safiyar ranar Lahadi a mujami'ar First Baptist na yankin Sutherland Springs wanda ke da nisan kilomita 35 daga kudu maso gabashin San Antonio na jihar Texas. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China