Rahotanni na cewa, a jiya ne shugaban kasar Koriya ta Kudu Moon Jae-in ya bayyana cewa, babban burin kasarsa shi ne shimfida zaman lafiya a fadin zirin Koriya, maimakon kai hare-hare a yankin. Ya ce an kakaba wa kasar Koriya ta Arewa takunkumi ne da nufin ganin ta dawo teburin shawarwari ba domin matsa mata lamba ba. (Maryam)