in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin tana fatan Koriya ta kudu za ta ci gaba da daidaita batun THAAD yadda ya kamata
2017-11-23 11:11:03 cri
Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya ce, yana fatan kasar Koriya ta kudu za ta daidaita batun na'urorin kandagarkin makamai masu linzami sanfurin THAAD yadda ya kamata.

Mr Wang wanda ya bayyana hakan yayin tattaunawarsa da takwararsa ta kasar Koriya ta kudu Kang Kyung-wha, ya ce kasar Sin tana martaba alkawaru uku da Koriya ta Kudu ta yi, wadanda ke cewa, ba za ta yarda a sake girke wasu na'urorin ba, sannan ba za ta shiga kawancen da Amurka ke jagoranta game da girke wadannan na'urori ba, haka kuma ba za ta karfafa kawancen sojojin dake tsakaninsu da Amurka da kuma Japan ba, haka kuma ba ta da niyyar kawo wata barazana ga muradun tsaron kasar Sin.

Jami'in na kasar Sin ya kuma buakci sassan biyu, da su hada kai, don karfafa fahimtar juna, da rage bambance-bambancen dake tsakaninsu, da samar da yanayin da ya dace na sake dawo da akalar dake tsakaninsu.

A nata jawabin Madam Kang ta ce, a shirya kasarta ta ke ta dawo da huldar dake tsakaninsu,kana za ta ci gaba da karfafa musaya da tuntubar juna tsakanin al'ummomi da manyan jami'an kasashen biyu, kamar yadda ke kunshe cikin sanarwar da sassan biyu suka fitar da kuma ganawar baya-bayan da shugabannin kasashen biyu suka yi.

Rahotanni na cewa, an samu ci gaba a dukkan fannoni , duk da tafiyar hawainiya da aka fuskanta a dangantakar sama da shekaru 25 tsakanin kasashen biyu.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China