in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ta damu matuka game da gwajin makami mai linzami da DPRK ta yi
2017-11-29 19:42:25 cri
Kasar Sin ta bayyana cewa, ta damu matuka kana ba ta goyon bayan sabon gwajin makami mai linzamin da ka iya kaiwa wata nahiya da kasar Koriya ta yi.

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Geng Shuang wanda ya bayyana hakan Larabar nan yayin taron manema labarai da aka saba yi a nan birnin Bejing, ya ce kasar Sin ta bukaci Koriya ta arewa da ta martaba kudurorin kwamitin sulhu na MDD, kana ta yi watsi da duk wani mataki da zai kara tsananta halin da ake ciki a zirin koriya.

A yau da safe ne gidan Talabijin na Koriya ta arewan ya ba da rahoton cewa, kasar ta yi nasarar gwada harba wani makami mai linzami da ta kera wanda ka iya kaiwa wata nahiya.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China