in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ta sake jaddada matsayinta a kan batun nukiliyar Koriya
2017-11-08 20:44:44 cri
Kakakin ma'aikatar harkokin waje ta kasar Sin Hua Chunying ta ce, Sin na fatan sassa masu ruwa da tsaki, za su yi kokarin sassauta halin da ake ciki a zirin Koriya, tare kuma da maido da batun nukiliyar zirin Koriya a teburin shawarwari.

Kakakin ta fadi haka ne a taron manema labarai da aka yi a yau Laraba a nan birnin Beijing.

Ta kuma jaddada cewa, har kullum Sin na aiwatar da kudurin kwamitin sulhu na MDD a game da zirin Koriya yadda ya kamata, musamman ma tanade-tanaden da suka shafi abubuwan da kudurin ya haramta. (Lubabatu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China