in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kasar Botswana ya nanata muhimmancin amfani da ilmi wajen gina tattalin arzikin kasa
2017-12-10 12:58:21 cri
Shugaban kasar Botswana Seretse Khama Ian Khama ya bayyana cewa gwamnatinsa a shirye take ta sauya fasalin hanyar samun tattalin arzikinta ta hanyar amfani da ilmi, maimakon tsohuwar hanyar da kasar ta dogara da ita wajen samun tattalin arziki.

Khama ya bayyana hakan ne a lokacin da ya halarci bikin yaye daliban kwalejin akantoci ta Botswana BAC na shekarar 2017, a Gaborone, babban birnin kasar.

Ya jadda cewa, muddin kasar tana fatar samun sauyi, akwai bukatar a canza fasalin tsarin ilmin kasar wanda ta haka ne za'a kara zurfafa tunani, da kirkire kirkire, da sana'o'in dogaro da kai, da kuma ingantaccen tsari.

Khama ya ce, ya kamata a sauya fasalin tsarin ilmin manyan makarantun kasar ta yadda za su dinga samar da 'yan kasa masu kwarewa ta kowane fanni.

Ya kara nanata aniyarsa inda ya buga misali da shirin muradun ci gaban karni na UNESCO nan da shekarar 2030 mai taken "Yadda za'a shigar da kuma samar da ingantaccen ilmi wanda zai zama abin koyi ga rayuwar dukkan bil adama."

Ya bayyana cewar wannan muhimmiyar hanya ce da za ta kara daga darajar ilmi, da samun kwarewa, da inganta halayyar 'yan kasa ta yadda za su kasance masu amfanar da kansu da kasarsu har ma da duniya baki daya.

Khama, wanda yake shirin sauka daga karagar shugabancin kasar ta Botswana a badi ya nanata cewa, ba ya tantama cewa kwalejin BAC ta yi namijin korari a shekaru da dama wajen ganin ilmomin da take samarwa sun kasance masu muhimmanci wadanda za su cimma burikan da aka sanya gaba. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China