in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Botswana ta karbi bakuncin taron jami'an Afrika na 2017
2017-08-04 10:30:33 cri
Gwamnonin manyan bankunan duniya, da na hukumar ba da lamini ta IMF, da wakilai daga kasashen Afrika, sun fara taron shugabannin Afrika na 2017 a Gaborone a ranar Alhamis.

Taron na wuni biyu mai taken: "Sauya fasalin tattalin arziki da samar da ayyukan yi: Ta hanyar mayar da hankali kan aikin gona da kasuwancin kayan amfanin gona."

Wakilan sun hada da ministocin kudi da gwamnonin manyan bankunan kasashen Afrika 54, za su tattauna ne game da muhimman batutuwa da suka shafi fahimtar juna da daukar matsaya game da ta'ammalin da manyan cibiyoyin kudi na kasa da kasa.

Taron na masu ruwa da tsaki, ya kasance wata dama ce da kasashen Afrika ke amfani da ita wajen bayyana matsayinsu game da sha'anin yin mu'amala da juna wajen daukar ajandoji mafiya muhimmanci da za su bunkasa ci gaban nahiyar.

Da yake kaddamar da bude dandalin a hukumance, shugaban na kusoshin Afrika, Kenneth Matambo wanda kuma shi ne ministan kudi da tattalin arziki na kasar Botswana, ya bayyana cewa, sun zabi tattaunawa game da rawar da aikin gona zai iya takawa wajen farfado da tattalin arziki da samar da ayyukan yi, musamman ga mata da matasa, wadanda su ne suka fi fama da matsalar koma bayan tattalin arziki.

Matambo, ya bayyana cewa, a matsayinsu na shugabannin gwamnatocin Afrika za su ci gaba da yin aiki tare karkashin ajandar dauwwamammen ci gaba na kungiyar tarayyar Afrika nan da shekara ta 2063, inda za su aiwatar da shirin aikin gona na zamani. Sannan ya jaddada cewa za su yi amfani da kimiyya da fasaha, da kirkire kirkire da ilmin da 'yan kasashen ke da shi domin samar da riba da abubuwan ci gaba masu daukar hankali a Afrika. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China