in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shirin sada zumunta tsakanin jama'ar Sin da kasashen Afrika ya karkata ga raya karkara a Botswana
2015-08-06 11:01:50 cri
A ranar Talata ne aka gudanar da wani aikin sada zumunta tsakanin jama'ar Sin da na kasashen Afirka a kauyen Conway dake kudancin kasar Botswana, aikin da ya shafi taimakawa matalauta a fannin noma.

Kungiyar kamfanonin kasar Sin da ke kasar Botswana, da hadin gwiwar kwamitin raya aikin gona na kauyen Conway ne suka shirya wannan aiki, inda ake sa ran kasar Sin za ta bayar da kudade na taimako ga mutanen da ke kauyen, domin su gyara gonaki da fadinsa ya kai eka 40, ta yadda jama'ar wurin za su iya yin amfani da albarkatun gonakin su yadda ya kamata wajen shuke-shuke, da gudanar da aikin ban ruwa, don samun karin kudaden shigarsu.

A yayin bikin, ministan aikin gona na kasar Botswana Kangwe Patrick Ralotsia, ya ce wannan aiki na sada zumunta tsakanin jama'ar kasar Sin da na kasashen Afrika zai haifar da moriya ga al'ummar kauyen Conway, kuma zai kara dankon zumunci da ke tsakanin jama'ar kasashen biyu, da ciyar da dangantakar bangarorin biyu gaba.

Mukaddashin ofishin jakadancin Sin da ke kasar Botswana Li Nan ya ce, Sin tana fatan hadin gwiwa tare da kungiyar kamfanonin Sin da ke Botswana wajen taimakawa al'ummar dake kauyen Conway. Kana ya yi imanin cewa jama'a za su ci gajiya daga wannan aiki.

Ya ce gwamnatin Sin da aikin sada zumunta tsakanin jama'ar kasashen biyu, za su ci gaba da kara kwazo wajen raya zamantakewar al'ummar kasar. (Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China