in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ana cikin wani lokaci mai muhimmanci a kokarin hana yaduwar cutar AIDS a Botswana, in ji jami'in MDD
2015-07-28 11:16:57 cri
Jami'i mai kula da aikin hulda da gwamnatoci na hukumar yaki da cutar kanjamau ta MDD (UNAIDS) Sun Gang, ya ce, kasar Botswana wadda ke kan gaba tsakanin kasashe masu tasowa a kokarin da ta ke na dakile cutar kanjamau, tana cikin wani yanayi mai muhimmanci ta fuskar aikin, wadda kuma za ta fuskanci wasu kalubaloli da barazana.

Sun Gang ya fadi haka ne yayin hira da wakilin kamfanin dillancin labaru na Xinhua a kwanakin baya. A cewarsa, Botswana wadda ke bayan Swaziland da Lesotho, ta kasance kasa ta uku da al'ummarta ke yawan kamuwa da cutar kanjamau.

Sakamakon wani binciken da aka gudanar a shekarar 2013 ya sheda cewa, kashi 16.8% na al'ummar kasar suna dauke da kwayoyin cutar kanjamau, yayin da kaso 50.5% cikin matan da shekarunsu ke tsakanin 35 da 39 ke dauke da cutar.

Sai dai mista Sun ya ce, hukumar yaki da cutar ta AIDS da ke kasar Botswana ta yi ayyuka da yawa don yaki da cutar, inda gwamnati ta zuba kudin da ya kai kashi 60 zuwa 70% na dukkan kudin da aka tattara a kasar don dakile cutar kanjamau.

Bayanai na nuna cewa, aikin yaki da cutar ya fi dogaro kan kudaden da gwamnati kan samar idan aka kwatanta da sauran kasashen Afirka. Sa'an nan kasar ta kasance kasa ta farko a nahiyar Afirka da ta alkawarta samar da jinya kyauta ga mutanen da suka kamu da cutar kanjamau.

Amma yayin da ake samun ci gaba a fannin yaki da cutar kanjamau, Botswana tana ci gaba da fuskantar matsala a fannin rigakafin cutar. A cewar Sun Gang, nazarin da aka gudanar cikin shekaru 10 da suka wuce ya sheda yadda ba a mai da hankali sosai kan matakan samar da kariya yayin jima'i. Ban da haka kuma, mutanen da suka yi gwajin matsayin su ba su da yawa a kasar, kana ba a ilimantar da samari da 'yan mata a kasar sosai ba dangane da matakan hana kamuwa daga cutar kanjamau.(Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China