in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kasar Botswana ya bukaci a tabbatar da hadin kan kasar
2017-10-01 12:58:01 cri
A ranar Asabar ne, al'ummar kasar Botswana suka yi bikin murnar samun 'yancin kan kasar shekaru 51, inda shugaban kasar Seretse Khama Ian Khama yayi kira ga jama'ar kasar da su tabbatar da hadin kan kasa.

A sakon da ya gabatar na bikin murnar cikar kasar shekaru 51 da samun 'yancin kai a babban birnin kasar Gaborone, Khama, ya bayyana ranar bikin a matsayin wani muhimmin lokaci da al'ummar kasar Botswana zasu yi amfani da shi wajen girmama juna da kuma tabbatar da hadin kan kasar.

Yace an kafa tsarin zamantakewar al'ummar Botswana shekaru masu yawa da suka shude a bisa girmama juna, da hadin kan kasa, da kuma bin dukkan matakan da suka dace wadanda zasu kawo cigaban kasar, da kuma magance wasu daga cikin manyan kalubalolin dake addabar fannin tattalin arziki da zamantakewar al'umma.

Botswana ta samu 'yancin kanta ne daga kasar Birtaniya a ranar 30 ga watan Satumbar shekarar 1966.

Shugaba Khama yace, abu mafi muhimmanci da ya kamata jama'ar kasar su lura da shi shi ne, ya kamata su yi watsi da dukkan wasu banbance bambance dake tsakaninsu wanda zasu iya haifar da samun rabuwar kawuna a tsaknain jama'ar kasar.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China