in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kudaden jarin kamfanonin kasashen waje da suka zuba a Sin ya samu tagomashi a watan Oktoba
2017-11-15 10:25:40 cri
Kudaden jarin kamfanonin kasashen waje da suka zuba a kasar Sin wato FDI, ya samu karuwar kashi 5 bisa 100 a watan jiya bisa makamancin lokacin shekarar bara, inda ya tasamma yuan biliyan 60.12 kwatankwacin dalar Amurka biliyan 9.05.

Wata kididdiga da ma'aikatar ciniki ta kasar Sin ta fitar a jiya Talata ta nuna cewa, an dan samu raguwar kudaden zuba jarin idan aka kwatanta da watan Satumba a lokacin da FDI din ya karu zuwa kashi 17.3 bisa 100.

A watanni 10 na farkon bana, jarin na FDI a kasar Sin ya kai yuan biliyan 678.7, inda ya karu da kashi 1.9 a makamancin lokacin a shekarar da ta gabata, kana ya zarta karin kashi 1.6 bisa 100 tsakanin watannin Janairu zuwa Satumba.

FDI na bangaren masana'antu yana ci gaba da karuwa yayin da masana'antun dake amfani da manyan fasahohin zamani da kamfanonin dake bada hidima su ne suka fi samun bunkasuwa cikin sauri.

Daga watan Janairu zuwa Oktoba, bangaren ba da hidima ya tasamma yuan biliyan 470.52, ko kuma kashi 69.3 bisa 100. FDI a bangaren samar da lantarki da iskar gas da ruwa ya karu zuwa kashi 74.3 bisa 100 idan aka kwatanta da makamancin lokacin a bara.

Kimanin yuan biliyan 56.65 ne aka samu a fannin manyan fasahohin masana'antu, watau ya karu da kashi 22.9 bisa 100 idan aka kwatanta da makamancin lokacin a bara.

Manyan fasahohin kamfanonin bada hidima sun yi amfani da yuan biliyan 95.01 na FDI, inda ya samu karin kashi 20 bisa 100 idan aka kwatanta da makamancin lokaicn a bara. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China