Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya jaddada bukatar rungumar manufofin da za su bunkasa tattalin arzikin kasa a shekarar 2018 dake tafe.
Shugaba Xi ya bayyana hakan ne, yayin taron karawa juna sani da ya gudana a nan birnin Beijing, tare da wakilan jam'iyyun da ba na kwaminis ba, da ma wakilai daga bangarorin da ba 'yan siyasa ba ne a kasar.
Xi wanda kuma shi ne babban sakatare na kwamitin kolin JKS, ya kara da cewa, yanayin tattalin arziki da ake ciki yanzu haka a kasar Sin na kan wata gaba, ta sauyi daga saurin bukasa zuwa ci gaba mai karko.
Ya ce nan gaba kadan, ci gaba mai karko zai zamo jigon cimma bukatun kasar Sin a fannin bunkasuwa, da ma hanyoyin tsara cimma hakan, tare da dabarun aiwatar da raya sassan tatttalin arziki mai fa'ida ga al'umma.
Shugaban na Sin ya ce, cimma nasarar bunkasuwa mai karko na da muhimmancin gaske ga al'ummar kasar Sin, domin hakan zai ba da damar dorewar ci gaba mai ma'ana, da tattalin arziki mai alfanu ga al'umma baki daya.
Kaza lika shugaba Xi ya ce ya zama wajibi a kau da tunanin 'yan kasa daga abubuwan da ka iya haifar da rudu, ya zuwa al'amura masu samar da managarcin tunani da wayewar kai.(Saminu Alhassan)