Tuni dai aka fidda manufar yafiyar harajin cikin sanarwa, wadda ma'aikatar cinikayyar kasar ta Sin ta dora a yanar gizo.
Bisa tanajin manufar gwamnatin kasar ta Sin, masu shigar da nau'o'in kayayyakin da suka shafi bunkasa fasaha, za su samu ragi na kusan dalar Amurka miliyan 350, sakamakon yafiyar harajin da za a yi masu, kamar dai yadda wannan sanarwa ta bayyana. (Saminu Hassan)