Sanarwar ta kara da cewa, daga yanzu za a kara samar da kariya kan yadda ake gudanar da harkokin kasuwanci da ma 'yancinsu na mallakar fasaha, kana a hannu guda su ma kamfanoni masu zaman kansu za su ci gajiyar da kamfanonin gwamnatin ke samu na kariyar 'yancin mallakar fahasa.
Haka kuma sanarwar ta ce, za a kara kare 'yancin mallakar fasaha na kayayyakin cikin gida, za kuma a rika a daidaita laifukan da suka shafi tattalin arziki kamar yadda dokoki suka tanada.
Idan ba a manta ba, muhimmin rahoton da aka gabatarwa taron wakilan JKS karo na 19, ya bayyana cewa, wajibi ne gyare-gyaren da ake aiwatarwa a fannin tattalin arziki ya mayar da hankali kan inganta tsarin kare 'yancin mallakar fasaha da tabbatar da a sakarwa kasuwa mara game da yadda za a rika samar da kayayyaki.
Rahoton aikin gwamnati na wannan shekara, ya bayyana cewa, kare 'yancin mallakar fasaha na nufin kare 'yan kwadago, kirkire-kirkire, da karewa da kuma samar da tsarin ma'aikata masu inganci.(Ibrahim)