Kimanin dakarun wanzar da zaman lafiya 'yan kasar Ugandan 12 ne mayakan Al-Shabaab suka hallaka a Somaliya, kana wasu dakarun 9 kuma aka raunata.
Birgediya Richard Karemire, mai magana da yawun rundunar sojin kasar Uganda ya shedawa 'yan jaridu cewa, mutuwar abokan aikin nasu ba zai sanyaya musu gwiwa ba wajen murkushe mayakan kungiyar ta Al-Shabaab.
A ranar Talata ne rundunar sojin kasar Ugandan ta kafa hukumar binciken musabbabin mutuwar dakarun.
Kasar Uganda ta bada gudumowar sojoji kimanin 6,500 daga cikin adadin sojojin kiyaye zaman lafiya 22,000 na tarayyar Afrika dake aiki a Somalia. (Ahmad Fagam)