Masu aikin hakar sabon sinadarin iskar gas dangin hydrates a kasar Sin, sun kammala aikin gwaji na kwanaki 60 a tekun kudancin kasar, aikin da ya bude sabuwar kofar bincike, game da samar da sabon nau'in makamashi mai tsafta.
An dai fara aikin ne tun a ranar 10 ga watan Mayun da ya shude, a yankin kogin Pearl, inda aka samu tarin wannan sinadari sama da wanda aka taba samu a wasu sassa na duniya, kamar dai yadda hukumar safiyon albarkatun kasa ta kasar Sin ta bayyana.
Hukumar ta ce, yayin wannan aiki, an hako sinadarin iskar gas na Methane da yawan sa ya kai kubik mita 300,000, wanda hakan ke nuna cewa, a kullum ana hako kimanin kubik mita sama da 5,000 ke wannan sinadari.
Kasar Sin ta bayyana nasarar fara wannan aiki mai muhimmanci ne tun a ranar 18 ga watan Mayu. Lamarin da kuma ake fatan zai ba da gudummawa ga kara cin gajiya daga iskar gas ta wannan sabuwar fasaha.(Saminu)