Abu-Ajela Ammar, shi ne kwamandan rundunar 'yan sanda masu tsaron bakin tekun ya bayyana cewa, lokacin da jami'an sintiri suka isa wurin, kwale-kwalen ya riga ya kife, inda aka gano gawawwaki da dama, tare kuma da wasu bakin hauren dake cikin ruwa, wadanda ba su da koshin lafiya. Bisa labarin da aka samu an ce, musabbabin kifewar kwale-kwalen shi ne, ya dauko fasinjoji fiye da kima.
Abu-Ajela Ammar ya kara da cewa, jami'an sintiri sun kara gano wani kwale-kwalen roba mai dauke da bakin haure guda 120, yayin da suka dauko bakin hauren da suka tsallake rijiya da baya zuwa sansanin sojan ruwa dake birnin Tripoli.
Tun daga shekara ta 2011 zuwa yanzu, halin da ake ciki a kasar Libya ya kara ta'azzara, inda gwamnatin kasar ba ta iya kulawa da bakin tekun kasar yadda ya kamata, lamarin da yasa wasu bakin hauren suka ratsa ta kasar Libya, suka tsallaka Bahar Rum har suka isa kasashen Turai. (Murtala Zhang)