A kwanakin nan ne tawagar MDD dake kasar ta Libya ta shirya tattaunawa a kasar Tunsiya tsakanin wakilan jam'iyyun siyasar kasar ta Libya domin yiwa yarjejeniyar siyasar gyaran fuska, matakin farko da wakilin tawagar MDD dake Libya Ghassan Salame ya dauka a watan Satumban wannan shekara da nufin kawo karshen bambance-bambancen siyasar da kasar ke fuskanta.
A ranar Talatar da ta gabata ce majalisar dokoki dake gabashin kasar ta amince da shawarar da MDD ta gabatar na aiwatar da wannan gyara, sai dai kuma abokiyar adawarta ta yi watsi da wannan shawara, inda ta sanar da yiwuwar shirya zabuka cikin watanni shida domin kafa gwamnati mai kunshe da masana.
Masu sharhi na cewa, wannan mataki tamkar mayar da hannu agogo baya ne, a kokarin da ake na kawo karshen dambarwar siyasar kasar, lamarin da ka iya kaiwa ga samun gwamnati ta uku, bayan biyun da ake da su yanzu haka.
Kasar Libya dai ta tsunduma cikin rikicin siyasa ne, tun bayan boren shekarar 2011 wanda ya kai ga hambarar da gwamnatin marigayi Gaddafi, lamarin da ya haifar da rudani da matsalar tsaro a kasar.(Ibrahim)