Wanga wanda mamba ne a zaunannen kwamitin hukumar siyasa ta kwamitin kolin JKS, ya ce muddin ana bukatar a biya bukatun jama'a na samun rayuwa mai inganci a sabon zamanin da ake ciki da kuma kasa mai hankoron kirkire-kirkire, wabiji ne a kawar da wadannan matsaloli.
Jami'in na kasar Sin wanda ya bayyana hakan yayin taro na 12 na kungiyar yaki da masu satar mallakar fasaha da yin jebun kayayyaki ta kasa, ya ce ko da yake ba a kai ga magance wadannan matsaloli baki daya ba, amma yanzu haka yanayin kasuwa da matakan kare muradun masana'antu da masu sayayya sun inganta, biyo bayan nasarar da aka samu wajen magance wadannan matsaloli, kuma nan ba da dadewa ba za su zama tarihi.
Wang ya ce kasar Sin za ta ci gaba da daukar matakan ganin an magance matsalar masu satar mallakar fasaha da jebun kayayyaki da ake fitarwa zuwa kasashen dake kan hanyar ziri daya da hanya daya, ta yadda za a kare martabar kayayyaki kirar kasar Sin. (Ibrahim)