Katafaren kamfanin cinikayyar yanar gizo na kasar Sin Alibaba, ya sanar da samun kudaden da suka kai sama da dalar Amurka biliyan 2.62 kimanin kaso 146 cikin 100 a rubu'i na biyu na wannan shekara.
Rukunin kamfanin na Alibaba wanda ya sanar da hakan a yau Alhamis ya ce, ribar da kamfanin ya samu ta kai Yuan biliyan 55 a rubu'in farko na wannan shekara, wato sama da kaso 61 cikin 100 bisa makamancin lokaci na bara.(Ibrahim)