in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Najeriya ya bayyana tabbacin kawo karshen rikicin siyasar Liberiya
2017-11-22 10:30:20 cri
Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya ya bayyana tabbacin cewa, za a warware dambarwar siyasar kasar Liberiya kamar yadda kundin tsarin mulkin kasar ya tanada.

Shugaba Buhari ya ba da wannan tabbaci ne jiya Talata a Abuja, fadar mulkin kasar ta Najeriya, yayin da ya tarbi takwaransa na kasar Togo, kana shugaba kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka (ECOWAS) na wannan karo Faure Gnassingbe .

Shugaban Najeriyar ya kuma bukaci dukkan bangarorin da abin ya shafa, da su kai zuciya nesa, yayin da ake jiran hukuncin da kotun kolin kasar za ta yanke game da wannan lamari. Yana mai fatan cewa,dukkan bangarori za su amince da sakamakon hukuncin kotun,domin tabbatar da mika mulki cikin lumana.

A nasa jawabi shugaban kungiyar ta ECOWAS Faure Gnassignbe, ya ce, ya sha ganawa da shugaba Buhari don neman shawararwarin sa kan yadda za a magance kalubalen da yankin yammacin Afirka ke fuskanta.

Rikicin siyasar kasar Liberia dai ya kunno kai ne, sakamakon zargin tabka magudi a zagayen farko na zaben ranar 10 ga watan Oktoba da ya gudana a kasar.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China