in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugabannin kasashen Sin da Amurka za su raya makomar dangatakarsu
2017-11-04 12:51:10 cri
Mataimakin ministan harkokin wajen Sin Zheng Zeguang, ya ce ana sa ran ganawa tsakanin shugaban kasar Sin Xi Jinping da takwaransa na Amurka Donald Trump, da za a yi a birnin Beijing mako mai zuwa, zai fiddo da tsare-tsaren raya dangantakar dake tsakanin kasashen a wani sabon zamani.

Yayin wani taron manema labarai a jiya, Zheng Zeguang ya ce kasar Sin da Amurka na kokarin ganin ziyarar Donald Trump a kasar Sin ta cimma nasara.

Donald Trump da zai kawo ziyara kasar Sin daga ranar 8 zuwa 10 ga wannan watan, zai zama shugaban kasa na farko da zai kawo ziyara kasar tun bayan kammala babban taron JKS karo na 19.

Mataimakin ministan ya kara da cewa, baya ga abubuwa da za a gudanar a hukumance domin ziyarar, za a shirya wata ganawa ta daban tsakanin shugabannin biyu.

Bisa amfani da wannan dama, shugaba Xi Jinping da Donald Trump, za su yi muhimmiyar tattaunawa kan muhimman batutuwa da suka shafe su tare da cimma matsaya da inganta fahimtar juna da abota tare da habaka dangantakar dake tsakaninsu a dukkan fannoni.

Ya ce jigon dangantakar tattalin arziki tsakanin kasashen biyu shi ne morar juna. Inda ya ce cike gibin harkokin cinikayya tsakanin Sin da Amurka na bukatar Amurka ta fadadad fitar da kayayyaki zuwa kasar Sin da kara zuba jari tsakaninsu, maimakon haramta shigar kayayyaki daga kasar Sin.

Bugu da kari, Zheng Zeguang ya ce, cacar bakin cinikayya za ta yi illa ga kasashen, yana mai cewa kasashen biyu abun sha'awa ne kuma suna da dimbin damarmaki na hadin gwiwa. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China