A sanarwar da kakakin MDD Stephane Dujarric ya yi wa taron manema labarai a helkwatar MDDr dake birnin New York ya ce, mista Guterres ya sha yin gargadi kan daukar wannan mataki, wanda yake ganin lamari ne da zai iya gurgunta yunkurin warware takaddamar dake tsakanin sassan biyu.
A ranar Talata ne, shugaba Trump ya shedawa Isra'ila da shugabannin kasashen Larabawa cewa, ya daura aniyar dauke ofishin jakadancin Amurka a Isra'ila daga birnin Tel Aviv zuwa Jerusalem, matakin da ake ganin ka iya haifar da tashin hankali a yankin.
A yau Laraba ne kuwa, ake sa ran Trump zai bayyana matsayar da ya dauka kan wannan batu. (Ahmad Fagam)