in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD ta yi Allah wadai da matakin Amurka na janyewa daga yarjejeniyar bakin haure
2017-12-04 10:04:27 cri
Shugaban babban taron MDD Miroslav Lajcak, ya nuna takaici dangane da matakin da Amurka ta dauka na janyewa daga yarjejeniyar da ta shafi bakin haure, wanda MDDr ke jagoranta don samar da kariya, da kuma tsara dokoki da suka shafi makaurata.

Sashen dake kula da hulda da MDD na kasar Amurka, ya sanar da babban sakataren MDD Antonio Guterres cewa, gwamnatin shugaba Trump ta riga ta zartar da hukuncin janyewa daga kashin farko na shirin yarjejeniyar MDD na hadin gwiwar kasa da kasa na shekarar 2018 game da batun kula da bakin haure.

Ya ce rawar da Amurka za ta taka game da batun bakin haure yana da matukar tasiri, bisa la'akari da yadda Amurkar a bisa tarihi take yin maraba da bakin haure daga sassan duniya daban daban. Don haka kasar tana da kwarewa da fahimtar yadda za ta bada taimako dangane da yadda za'a aiwatar da shirin cikin nasara.

Lajcak ya nanata cewa, batun bakin haure matsala ce da ta shafi duniya baki daya wanda take bukatar kasashen duniya su hada hannu wajen warware ta, kana hadin gwiwar kasa da kasa ita ce babbar hanyar da za'a bi wajen shawo kan wannan babban kalubalen. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China